Isa ga babban shafi
Faransa

An yi zazzafar muhawara tsakanin Macron da Le Pen kan zaben Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da abokiyar fafatawar sa wajen takarar shugabancin kasar Marine Le Pen sun yi zafafan kalamai dangane da dangantakar kasar da Rasha da kuma batun sanya dankwali a mahawarar da suka tafka daren ranar Laraba da zummar janyo hankalin masu kada kuri’u.

Shugaba Emmanuel Macron yayin muhawara da babbar abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen kan neman lashe zaben shugabancin kasar Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron yayin muhawara da babbar abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen kan neman lashe zaben shugabancin kasar Faransa. © AFP / LUDOVIC MARIN
Talla

Daga cikin abubuwan da suka ja hankali a mahawarar da aka kwashe tsawon sa’oi uku ana tafkawa, akwai bayanain da Le Pen ta yi cewa za ta haramta wa mata musulmi sanya lullubi a bainar jama'a, shirin da Macron ya ce ya saba wa ka’idojin da Faransa ta kafa kuma zai haifar da yakin basasa a kasar da ke da yawan musulmi a yammacin Turai.

Le Pen ta kuma yi alkawarin kawo karshen cin hanci da rashawa da ‘yan cirani masu zuwa Faransa, tana mai cewa hakan na kara yin muni.

'Yar takarar mai ra'ayin mazan jiya ta yi kira ga masu kada kuri'a da ke kokawa da hauhawar farashin kayayyaki da su farga, inda ta bayyana kanta a matsayin zakara ko da yake Macron ya tambayeta yadda ta samu alkaluman tattalin arziki.

Ta ce shugabancin Macron ya bar kasar cikin rarrabuwar kawuna, tana mai bada misali da masu zanga-zangar Yellow Vest tare da cewa Faransawa kamata yayi su koma tsintsiya madaurin ki daya.

Jim kadan bayan muhawarar, wani binciken jin ra’ayin jama’a, ya ce kashi 59 cikin 100 na masu kallo sun kamsu da Macron, yayin da kashi 39 cikin 100 suka ki amincewa da abokiyar hamayyar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.