Isa ga babban shafi
Zaben Faransa

Macon ya samu goyon bayan wasu fitattun mawaka da 'yan fim

Wasu fitattun mawaka da masu shirye fina-finai na Faransa kimanin 500 sun sanar da goyan bayan su ga shugaban kasar mai ci Emmanuel Macron a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar dake tafe, suna masu yin tir 'yar 'Yar takara jam'iyyar masu tsatsauran ra'ayi Marine Le Pen sa suka kira ta da mai kyamar baki.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da abokiyar takararsa  Marine Le Pen
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da abokiyar takararsa Marine Le Pen © AP/Jean-Francois Badias/Daniel Cole/Montage RFI
Talla

Kwanaki 10 kacal kafin gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar na Faransa, wanda zai tabbatar da wanda zai jagoranci kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a kungiyar ta EU na tsawon shekaru biyar masu zuwa, kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa shugaba mai ci Emmanuel Macron na dan gaban abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen.

Yanzu haka ‘yan takarar biyu sun zafafa yakin neman zabe don jan hankalin magoya bayansu da na sauran ‘yan takara da suka gaza kaiwa zagaye na biyu, masamman Jean Luc Melanchon da ya zo na uku a zagayen farko na zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.