Isa ga babban shafi
Zaben Faransa

Macron da Le Pen na zawarcin kuri'un masu sassaucin ra'ayi

Yayin da ya rage kwanaki 10 gabanin zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Faransa, manyan ‘yan takara biyu dake shirin fafatawa Emmanuel Macron da Marine Le Pen na ci gaba da zawarcin ‘yan bangaren hagu, na masu sassaucin ra’ayi wadanda kuri’unsu ke da mahimmaci a zaben.

Marine Le Pen da Emmanuel Macron
Marine Le Pen da Emmanuel Macron REUTERS - SARAH MEYSSONNIER
Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron mai neman tazarce a wani wa’adi na biyu ya maida hankali yankin  Strasbourg, inda ya ziyarta ranar Talata a gabashin kasar, yankin da suka baiwa Jean-Luc Mélenchon, dan takarar jam'iyyar LFI na masu sassaucin ra’ayi kuri’u da suka kaishi matsayi na uku a zagayen farko na zaben.

Yayin da yau yake gangami a Havre dake arewa maso yammacin kasar, tungar tsohon Firayimminista Edouard Philippe.

Ita kuwa Marie Le Pen ta jam’iyyar RN mai tsatsauran ra’ayi, ta zayarci Avignon mai tazarar kilomita 800, da inda abokin karawarta Macron ke ziyara a Kudancin Faransa, nan ma daya daga cikin manyan mazabu ne da suka baiwa Melenchon nasarar zama na uku, ko da yake ya yi kira ga magobaya bayansa da kada su baiwa Le Pen ko da kuri’a daya, duk da cewa yankin masu tsatsauran ra’ayi ne bisa al’ada.

Ga 'yan takarar da ke neman shiga Fadar Elysée, samun goyan bayan dan takarar jam'iyyar LFI na ‘yan mazan jiya Jean-Luc Mélenchon nada mutukar muhimmaci, saboda matsayin sa na uku a zagayen farko a ranar Lahadi da kashi 22% na kuri'un da aka kada, biye da Marine Le Pen da ta samu sama da kashi 23 da kuma Emmanuel Macron da ya samu sama da kashi 27.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.