Isa ga babban shafi
Zaben Faransa

Manufar Le Pen kan Afrika ta janyo cece-kuce

Yayin da ake tunkarar zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar Faransa, masana siyasar duniya na ci gaba da yin tsokaci kan manufofin babbar ‘yar adawa Merine Le Pen kan kasashen Afirka.

Marine Le Pen
Marine Le Pen AP - Daniel Cole
Talla

Ta fuskar tattalin arziki, Faransa ta fuskanci tasgaro a Afirka sakamakon zuba jarin da kasashen China, Indiya, da Brazil ke yi a nahiyar.

Le Pen wadda ta kasance ‘yar tsatssauran ra’ayi masharhanta na ganinn cewa tafiyarta na iya zuwa daya da wasu shugabannin Afirka, musamman idan aka yi la’akari da yadda alaka ta yi tsami tsakanin Macron da wasunsu.

Idan ta samu nasara shin ko za ta sasanta alakar da ta baci tsakanin Macron da shugabannin mulkin soja a Mali Assimi Goita, ko kuma na CAR Faustin Touadera ko kuma na kasar Guinea Mamadi Doumbouya, da suke fatan shan kayen shugaban da suke ganin ya musu kudundune.

Ko da yake masana da dama sun fi karkatar akalar cewa  babu tsammanin daya daga cikin ‘yan takarar biyu, Macron ko Le Pen, ba zai canza komai ba a alakar Faransa da Afirka, musamman kasashen da ta yi wa mulkin mallaka.

Le Pen dai an fi bada karfin za ta iya gyara alaka ta kut da kut da ke tsakanin Faransa da Afirka, musamman wadanda ta yiwa mulkin mallaka, duba da alwashin da ta yi ranar 13 ga Afrilu ga shugaban Senegal Macky Sall, kan cewa za ta yi dukkkan mai yuwuwa don ganin kasarsa ta samu kujerarar dindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Abin dai jira shine, sakamakon zaben da za a gudanar na ranar 24 ga watan nan na Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.