Isa ga babban shafi
Faransa-Zabe

Yau ake rufe yakin neman zaben shugabancin Faransa

‘Yan takarar shugabancin kasa a Faransa, Emmanuel Macron da Marine Le Pen sun shiga sahun karshe  na yakin neman zabe a Juma’ar nan, inda suke fatan shawo kan miliyoyin masu zabe da ba su kai ga yanke hukunci a kan wa za su zaba ba, kafin cikar wa’adin dakatar da yakin neman zabe, gabanin zaben na karshe mako.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen. AFP - JULIEN DE ROSA,CHARLES PLATIAU
Talla

Dukkannin ‘yan takaran sun caccaki juna kafin ranar karshe ta yakin neman zabe , inda Le Pen ta bayyana yakinin cewa sakamakon kuri’ar da za a kada zai wofintar da na ra’ayoyin al’umma da ke nuna Macron a kan gaba gabanin zabe.

Ta kuma yi kakkausar suka  a game da shirin abokin hamayyar nata na tsawaita shekarun yin ritaya daga aiki daga 62 zuwa 65, shirin da shugaba Macron jingine bayan mummunanr zanga zanga  shekaru 2 da suka wuce.

A nasa bangaren, shugaba Macro ya ce Le Pen na kokarin yin ungulu da kan zabo a game da akidar tsatsauran ra’ayi da ke tsangwamar Musulmi, da wani shirin haramta sanya hijabi a bainar jama’a, ta wajen yin watsi da akidar Turai ta kare  hakkin kowane mahaluki.

Daga tsakiyar daren wannan Juma’a, ba za a bari wani dan takara ya gana da manema labarai, ko kuma raba kasidu, ko gudanar da wani yakin neman zabe ba har zuwa karfe 8 na safe agogon GMT, lokacin da za a fara dakon sakamakon zabe.

Masu sharhi dai sun ce masu kaurace wa zaben za su kai kaso 25 zuwa 30, musamman kuma daga masu sassaucin ra’ayi da jin dadin yadda Macron ke jan ragamar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.