Isa ga babban shafi

Faransawa na kada kuri’a a zagayen karshe na zaben majalisar dokoki

Faransawa na kada kuri’a a zagaye na karshe na zaben 'yan majalisar dokokin kasar, inda kawancen shugaba Emmanuel Macron na masu ra'ayin tsaka-tsaki ke kokarin dakile kalubalen da suke fuskanta daga sabon kawancen bangaren masu sassaucin ra’ayi.

Wasu Faransawa yayin kada kuri'unsu a zaben 'yan majalisar dokokin kasar zagaye na biyu.
Wasu Faransawa yayin kada kuri'unsu a zaben 'yan majalisar dokokin kasar zagaye na biyu. © REUTERS / ERIC GAILLARD
Talla

Masu hasashe dai sun ce za a iya sake gudanar da zaben da aka yi ne a makon da ya gabata,  inda aka samu karancin fitowar jama’a.

Zaben ‘yan majalisar dokokin na Faransa dai na da muhimmaci ga manufofin da shugaba Emmanuel Macron ke son cimma a wa’adinsa na biyu, bayan lashe zaben da yayi a cikin watan Afrilun da ya gabata.

Hasashen da wasu cibiyoyin nazarin siyasa suka fitar a baya bayan nan, ya nuna cewar gamayyar jam'iyyar shugaba Macron ta "Together" na kan hanyar samun nasarar lashe kujeru da dama a majalisar dokokin Faransa, amma mai yiyuwa ta samu kasa da kujeru 289 da ake bukata domin samun cikakken rinjaye.

Sabon kawancen jam'iyyar NUPES masu sassaucin ra’ayi ma dai na fatan ba da mamaki, yayin da ita ma shugabar masu tsatsauran ra'ayi Marine Le Pen ke sa  ran samun gagarumar nasara ga jam'iyyarta ta ‘National Rally’, wadda ke da kujeru takwas kacal a majalisar dokokin kasar mai barin gado.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.