Isa ga babban shafi

Zaben Faransa: Faransawa zasu sabinta majalisar dokokin kasar

A Faransa ,kusan wata daya da rabi da  gudanar da zaben Shugaban kasar, da ya  baiwa shugaba mai ci Emmanuel Macron  nasarar lashe zaben , a yau lahadi aka fara zaben yan majalisun dokokin kasar.

Katin zaben 'yan Majalisun  Faransa
Katin zaben 'yan Majalisun Faransa AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Zaben Faransa na yau na  a matsayin zakaren gwajin dafi ga Shugaba Emmanuel Macron,wanda  a karkashin jam’iyya mai mulkin kasar zai yi kokarin ganin ya  samu rinjaye a majalisar dokokin Faransa,wanda shaka babu hakan zai bas hi damar tafiyar da manufofin da yake da su ta fuskar siyasa  kamar yada ya dau alkawali a yakin neman zaben  da ya gabata.

Shugaban kasar Emmanuel Macron na ci gaba da fuskantar  suka daga wasu yan siyasa da Faransawa dake kalon sa a matsayin mutumen da ya durkusar da diflomasiyar Faransa a idanun Dunitya,yayinda masu goyan bayan sa ke ci gaba da kawo ta su goyan baya a siyasar Shugaba Emmanuel macron.

Sama da Faransawa milyan 43 ne suka karbi katunan zabe  domin sabinta wannan majalisa mai dauke da yan majalisu 577 inda ake da yan takara sama da dubu 6, zaben da za aje zagaye na biyu  ranar 19 ga watan yuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.