Isa ga babban shafi

Faransa na tuhumar Martinez kan zargin badakalar cinikin mutum-mutumin Fir'auna

Hukumomin Faransa sun tuhumi wani tsohon daraktan gidan adana kayan tarihi na Louvre da ke birnin Paris da laifin karkatar da kudade da kuma hada baki wajen boye asalin wasu kayayyakin tarihi da masu bincike ke zargin an fitar da su daga kasar Masar.

Gunkin Fir'auna Toutankhamon
Gunkin Fir'auna Toutankhamon REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Wata majiya dake kusa da masu bincike tace an gurfanar da Jean-Luc Martinez ne a wannan Laraba bayan da ya kwashe kwanakin hannun ‘yan sanda, inda aka yi masa tambayoyi tare da wasu kwararrun biyu dake da masaniya kan badakalar kayyayakin tarihin na kasar Masar, ko da yake sun tsiri daga tuhumar.

Gidan kayan tarihi mafi girma

Shidai gidan adana kayan tarihin na Louvre, mallakin gwamnatin Faransa, shine mafi girma a duniya, inda akalla baƙi miliyan 10 ke ziyara duk shekara, a kiyasin kafin bullar annobar Covid-19 kuma gida ne na nuna wasu manyan al'adun gargajiya na Yammacin Turai.

Martinez da ya shugabancin gidan tarihin tun daga shekarar 2013 zuwa 2021 yanzu haka shine jakadan hadin gwiwar kasa da kasa a fannin kayayyakin tarihi.

Ana tuhumarsa da kauda kai, kan badakalar wasu kayayyakin tarihi daga kasar Masar da wasu kasashen gabas ta tsakiya, wanda ake tunanin ya ƙunshi wasu ƙwararrun Faransa da dama.

Fir'auna Tutankhamun

An fara binciken tun cikin watan Yulin shekarar 2018, shekaru biyu bayan reshen Louvre da ke Abu Dhabi ya sayi wani mum-mutumin da ake dangantawa da daya daga cikin Fir'aunan baya-bayan nan wato Tutankhamun kan kudi da yakai Yuro miliyan takwas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.