Isa ga babban shafi
Faransa - Benin

Faransa ta yi bajakolin karshe kafin maida kayayyakin tarihin Benin

Katafaren gidan adana kayan tarihi Quai Branly dake  birnin Paris yayi baje-kolin wasu gwamman kayayyakin tarihi da dakarun Faransa suka kwaso daga kasar Benin a zamanin mulkin mallaka. Bayanai sun nuna cewa wannan shi ne karo na karshe da za a nuna kayayyakin tarihin a Faransa kafin a mayar da su ga kasar ta Benin.

Kayyakin tarihin Benin da Faransa ta kwashe a Benin lokacion mulkin Mallaka, lokacin da akayi bajakolisu a Paris, ranar 02 Oktoba 2007.
Kayyakin tarihin Benin da Faransa ta kwashe a Benin lokacion mulkin Mallaka, lokacin da akayi bajakolisu a Paris, ranar 02 Oktoba 2007. AFP - OLIVIER LABAN-MATTEI
Talla

Kwanaki shida aka shafe ana baje-kolin kayayyakin tarihin guda 26, daga cikin tarin abubuwan da sojojin Faransa suka kwace daga kasar Benin a shekarar 1892, kafin a sake jigilar su zuwa kasar da ke yammacin Afirka a karshen wannan watan.

Kayayyakin dai sun fito ne daga masarautar Dahomey da ke kudancin Benin a yau, cikinsu kuma har da gadon sarautar Sarki na karshe na Dahomey, Behanzin, da kuma wasu mutum-mutumi guda uku, da kuma kofofin fada guda hudu.

Wani rahoton tawagar kwararru da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kafa ya ce adadin kayayyakin Afirka dake gidajen tarihin Faransa sun kai akalla dubu 90,000.

Matakin mayar da wadannan kayayyaki ya biyo bayan kiraye-kirayen da ake yi daga Afirka kan neman kasashen Turai su mayar da ganimar da Turawan mulkin mallaka suka yashe daga gidajen tarihin yankunan da suka taba mamayewa a shekarun baya.

Tun bayan zabensa Shugaba Emmanuel Macron ke kokarin maido da kimar kasarsa a nahiyar Afirka, musamman a tsakanin matasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.