Isa ga babban shafi

Tsohon shugaban Faransa ya auri budurwarsa

Tsohon shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya auri budurwar sa da suka dade suna soyayya, Julie Gayet mai fitowa a shirin fina finai, wadda labarin soyayyar su yayi fice a shekarar 2014 lokacin da yake rike da mukamin shugaban kasa.

Tsohon shugaban Faransa Francois Hollande
Tsohon shugaban Faransa Francois Hollande AFP - PASCAL LACHENAUD
Talla

Jaridar La Montagne ta ruwaito Magajin Garin Tulle, Bernard Combes na fadin cewar an gudanar da kwarya kwaryar bikin auran ne a karshen mako, inda Hollande ya sanya kwat, yayin da amaryar sa ta sanya farar rigar da amare ke sanyawa a dakin taron da akayi bikin.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce ba’a bayyana irin mutanen da suka halarci bikin auran ba, wanda ya samu halartar mawaki Benjamin Biolay da ya taba aiki da amaryar Hollande a cikin wani shirin fim a shekarar 2021.

Tsohon shugaban wanda bai taba aure ba a rayuwar sa, yayi mu’amala da Gayet lokacin da yake rike da mukamin shugaban kasa, yayin da kuma yake neman Yar Jarida Valerie Trierweiler wadda ita ta taka rawa a matsayin maid akin shugaban kasa.

Hollande na da ‘yaya guda 4 da suka haifa da abokiyar zaman sa Segolene Royal, wadda ta taba tsayawa takarar shugaban kasar Faransa.

Amaryar Hollande, Gayet na da yara maza guda biyu da suka haifa da wani dan kasar Argentina, Santiago Amigorena mai rubuta wakoki da suka raba auran su a shekarar 2006.

Gayet wadda ta cika shekaru 50 a ranar juma’a kafin auran da suka yi ranar asabar, ta takaita bayyanar ta a bainar jama’a da Hollande lokacin da yake rike da mukamin shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.