Isa ga babban shafi
Faransa-Macron

Macron ya sha alwashin hada kan Faransawa bayan samun wa'adi na 2

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kudiri aniyar hada kan al’ummar kasar da ta tsunduma cikin matsalar rarrabuwar kawuna bayan da aka sake zabensa don yin wa’adi na 2 a zaben da masu tsatsauran ra’ayi suka zo kusa da lashe zabe a karon farko.

Emmanuel Macron wanda ya lashe zaben yin wa'adi na biyu a matsayin shugaban Faransa.
Emmanuel Macron wanda ya lashe zaben yin wa'adi na biyu a matsayin shugaban Faransa. AP - Christophe Ena
Talla

Da yake jawabin godiya ga dimbim magoya bayansa a kusa da Hasumiyar Eifel a daren Lahadi, shugaba Macron ya sha alwashin dinke barakar da aka samu a tsakanin Faransawa.

Macron mai ra’ayin tsakatsaki ya lashe zaben da kusan kaso 59 na jimillar kuri’un da aka kada, a yayin da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen ta samu  kashi 41 da digo 46, kamar yadda sakamakon karshe daga ma’aikatar cikin gidan kasar ya nuna.

Macron shine shugaban Faransa na farko a cikin shekaru 20 da aka zaba don yi wa’adi na 2, kuma nasarar ta faranta ran da dama a nahiyar Turai, ganin cewa an taka wa masu tsatsauran ra’ayi birki a kokarinsu na karbe mulki a kasar da ke  da mahimmanci a cikin kungiyar Tarayyar Turai.

Sai dai a wannan nasarar da ya samu a kan masu tsatsauran ra’ayi, tazarar ba ta da yawa  idan aka kwatanta da arangamar da suka yi a shekarar 2017, inda Macron ya lashe kashi 66 na jimillar kuri’un da aka kada, kuma sakamakon da Le Pen ta samu yanzu shine mafi armashi da masu tsatsauran ra’ayi suka taba samu a kasar.

Akwai gagarumin aiki a gaban Emmanuel Macron a wannan wa’adi na biyu da ya samu wadanda suka hada da shirin tinkarar zaben majalisar dokokin kasar a watan Yuni, wanda sai ya samu rinjaye zai iya aiwatar da manufofinsa, da  kuma batun neman mafita a game da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.