Isa ga babban shafi
Faransa- zabe

Shugabannin kasashen duniya na taya Macron murnar samun wa'adi na 2

Shugabannin Kasashen duniya sun fara aikewa da sakon taya murna ga shugaba Emmanuel Macron na Faransa sakamakon nasarar da ya samu domin yin wa’adi na biyu na shugabancin kasar a karawar da suka yi da Marine Le Pen.

Emmanuel Macron, shugaban Faransa.
Emmanuel Macron, shugaban Faransa. AFP - ERIC FEFERBERG
Talla

Shugaban Majalisar Turai Charles Michel yace nasarar Macron wata nasara ce ga Turai baki daya, domin ci gaba da aiki tare na karin shekaru 5, yayin da shugabar gudanarwar Turai Ursula von der Leyen ta bayyana cewar nasarar zata basu damar ci gaba da hulda tare.

Daga cikin shugabannin da suka aike da sakon taya murna akwai Firaministan Italia Mario Draghi wanda ya bayyana nasarar Macron a matsayin nasara ga daukacin kasashen dake nahiyar Turai.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya bayyana Faransa a matsayin makociyar su ta kusa, yayin da ya bayyana fatar ganin ya cigaba da aiki da shugaba Macron akan batutuwa da dama da zasu taimakawa kasashen biyu da kuma duniya baki daya.

Shima shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana farin cikin sa dangane da sakamakon, inda ya taya shugaba Macron murnar nasarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.