Isa ga babban shafi
Faransa-zabe

Macron ya lashe zaben Faransa don yin wa'adi na 2

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kama hanyar lashe zaben shugaban kasar zagaye na biyu da akayi yau lahadi domin yin karin shekaru 5 a karagar mulki.

امانوئل ماکرون
امانوئل ماکرون © AFP
Talla

Sakamakon farko da aka gabatar ya nuna cewar Macron ya samu tsakanin kashi 57.0 zuwa kashi 58.5 na kuri’un da aka kada, yain da abokiyar takarar sa Marine Le Pen mai ra’ayin rikau ta samu tsakanin kashi 41.5 zuwa kashi 43.0 na kuri’un.

Sakamakon zaben ya nuna raguwar banbancin tazara tsakanin yan takarar biyu kamar yadda aka gani a shekarar 2017 lokacin da suka fafata a tsakanin su a zagaye na biyu.

Amma duk da haka wannan nasara zata baiwa Macron damar ci gaba da jagorancin gwamnati da kuma aiwatar da manufofin san a Karin shekaru 5 masu zuwa.

Macron ya zama shugaban Faransa na farko da ya samu nasarar yin wa’adi na biyu tun bayan shugaba Jacques Chirac a shekarar 2002, yayin da shugaba Nicolas Sarkozy da Francois Hollande suka yi wa’adi guda guda.

Ana saran shugaban mai shekaru 44 yayi jawabi ga magoya bayan sa dangane da wannan nasara daren yau, yayin da abokiyar takarar sa Le Pen ke cewa yawan kuri’un da ta samu a zabe nasara ce a gare ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.