Isa ga babban shafi
Zaben Faransa

Macron da Le Pen za su yi muhawara mai zafi a yau

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen mai tsatsauran ra'ayi za su fafata a muhawarar da za a watsa ta gidan talabijin a yau Laraba, inda kowannensu ke fatan jan ra’ayin masu kada kuri’ar da basu yanke shawarar wanda za su zaba ba.

Marine Le Pen da Emmanuel Macron
Marine Le Pen da Emmanuel Macron © AP/Ludovic Marin/Pool/Montage RFI
Talla

Yanzu haka dai shugaba Macron ke kan gaba a zaben shugabancin kasar na Faransa bayan da ya lashe zagayen farko da fiye da kashi 27 na kuri’un da aka kada, sai dai masana siyasa makusantansa sun gargade shi da ya kaucewa tafka kuskuren yin sakaci kan burinsa na zarcewa kan wa’adi na biyu, a yayin muhawarar da zi fafata da Marine Le Pen a wannan Laraba.

Wasu zabukan jin ra’ayin jama’a da aka gudanar sun yi hasashen cewar shugaba Macron zai samu nasarar lashe zagaye na biyu na zaben da zai gudana nan da kwanaki 4 da ratar kusan kashi 10 na kuri’un da za kada kan mai tasttsauran ra’ayi Le Pen, wato maimaicin abinda ya faru zaben shekara ta 2017. Sai dai masu jefa kuri'ar da har yanzu ba su yanke shawara kan inda za su karkata ba ka iya sauya alkaluman.

Bayanai dai sun ce a bana jagorar ‘yan adawa Marine Le Pen ta maida hankali kan shirya wa muhawarar da za ta yi, don kaucewa abinda ya faru shekaru biyar da suka gabata, lokacin da rashin shirinta kan muhawarar ya taka rawa wajen shan kaye da ta sha a hannun shugaba Macron.

Muhawarar kai tsaye tsakanin ‘yan takarar shugabancin Faransa ta kasance al'adar siyasa a kasar tun daga shekarar 1974, lokacin da dan jam'iyyar gurguzu Francois Mitterrand ya yi takara da Valery Giscard d'Estaing. (Valeri Giskar Distar)

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.