Isa ga babban shafi

Macron ya dukufa wajen magance takaddamar shan kayi a majalisa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tattauna da shugabannin 'yan adawa domin kawo karshen takaddamar da ta biyo bayan rashin samun rinjaye a zaben 'yan majalisar dokokin kasar, bayan da ya ki amincewa da tayin murabus din da firaministar kasar ta yi.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa AP - Francois Mori
Talla

Macron ya gana da masu ra’ayin rikau, da kuma wasu shugabannin jam'iyyu na masu tsassauran ra’ayi irin su Marine Le Pen, yayin da yake neman mafita ga wani mawuyacin hali da ke barazanar jefa wa'adinsa na biyu cikin rikici watanni biyu bayan samun nasara a zaben shugabancin kasar.

Kazalika kallon gurguncewar siyasa da irin nasarorin da 'yan adawa irin su Le Pen suka samu, shi ma ya sanya ayar tambaya game da shugabancin Macron a nahiyar Turai, yayin da yake kokarin ci gaba da taka rawa wajen tunkarar mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

Firaministar Faransa Elisabeth Borne, wadda wasu manazarta ke zargin ta da hannu wajen gudanar da yakin neman zabe, ta mika wa Macron tayin murabus din ta, amma shugaban kasar ya ki amincewa da hakan.

Macron ya fara tattauanwar ne da Christian Jacob, shugaban jam’iyyar ‘yan mazan jiya, wato jam'iyyar da ta samu koma baya a watannin ‘yan watannin da suka wuce, amma a halin yanzu shugaban kasar zai iya nemansa don hada kai wajen samar da rinjaye a majalisar dokokin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.