Isa ga babban shafi

Macron-Le Pen- Makomar siyasar Faransa a Turai da Afrika

Yan takara biyu da za su kara a zaben shugabancin kasar Faransa na ranar lahadi mai zuwa Emanuel Macron da Marine Le Pen, sun tafka mahawara a cikin daren jiya, inda kowanne ya kare manufofinsa a game da siyasar cikin gida, alakar Faransa ta Afirka sai kuma matsayin kasar a cikin kungiyar Tarayyar Turai.

Yan takara Macron- Le Pen
Yan takara Macron- Le Pen AFP - NICOLAS TUCAT
Talla

Maharawar ta fara ne game da lamurran cikin gida a Faransa, inda Marine Le Pen ta jaddada matsayinta na haramtar sanya hijabi bainar jama’a matukar dai ta yi nasara a zaben ranar lahadi.

Yar takara Uwargida Marine Le Pen
Yar takara Uwargida Marine Le Pen AP - Michel Euler

Ta ce tana nan kan bakanta, cewa matukar ta yi nasara a zaben, ko shakka babu za ta haramta sanya hijabi bainar jama’a, Le Pen ta ce Hijabi wata sutura ce da masu tsatsauran ra’ayin islama suka tilasata wa jama’a,

Emmanuel Macron ya ce abokiyar hamayarsa na menan haddasa yakin basasa ne a kasar Faransa.Dokar raba kasa da batu ba wai yana nufin cewa ana yaki da wani addini ba ne, saboda inda na yi nasara a zabe ba zan haramta wa mata sanya hijabi ko mayafi ko alama da ke nuni da wani addini ba.

Shugaban Faransa kuma dan takara Emmanuel Macron
Shugaban Faransa kuma dan takara Emmanuel Macron © AFP

Emmanuel Macron na cewa ya gamsu da irin rawar da Faransa ke takawa a kungiyar Turai ta EU, ita kuwa Marine Le Pen ta ce za ta yi kokarin samar da sauyi ne game da manyan manufofin kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.