Isa ga babban shafi
Ukraine

An kashe mutane fiye da dubu 2 a birnin Mariupol

Gwamnatin Ukraine ta ce sama da mutane 2,100 aka kashe a birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa da sojojin Rasha suka yi wa kawanya tun lokacin da suka kaddamar da hare-hare kan garin.

Wani hoto da tauraron dan adam ya dauka da ke nuna yadda hare-haren sojojin Rasha suka ragargaza sassan birnin Mariupol na kasar Ukraine.
Wani hoto da tauraron dan adam ya dauka da ke nuna yadda hare-haren sojojin Rasha suka ragargaza sassan birnin Mariupol na kasar Ukraine. © Maxar Technologies/Handout via REUTERS
Talla

Cikin wani rahoto da ta wallafa a shafinta na Telegram, majalisar birnin ta Mariupol ta ce ya zuwa lokacin, mazauna garin Mariupol 2,187 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Rasha ke kaiwa.

Sanarwar ta ce kusan bama-bamai 100 dakarun Rasha suka harba cikin birnin, ciki har da wani farmaki da aka kai kan asibitin kula da mata masu juna biyu da na yara kanana a ranar Laraba, inda mutane akalla 17 suka jikkata.

Wasu rahotannin kuma sun ce an tare ayarin motocin agaji da suka nufi Mariupol a ranar Asabar, a wani shingen binciken ababan hawa da sojojin Rasha suka kafa, koda yake daga bisani dakarun sun kyale ayarin motocin.

Rasha ta ragargaza sansanin sojin Ukraine a kusa da Poland 

A wani labarin kuma, gwamnatin Ukraine ta ce, akalla mutane 35 ne suka mutu yayin da wasu 134 suka jikkata, a wani harin da jiragen yakin Rasha suka kai kan wani katafaren sansanin horas da sojojin Ukraine da ke kusa da iyakar Poland.

Da fari dai jami’ai sun ce mutane 9 suka rasa rayuakansu a farmakin, kafin daga bisani sun tabbatar da karuwar adadin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.