Ukraine ta ce a shirye take ta kare birnin Kyiv
Ukraine ta ce a shirye take ta kare babban birninta Kyiv, wanda ke fuskantar yiwuwar kawanya daga dakarun Rasha da ke dada kutsa kai, kuma suka ci gaba da luguden wuta a birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa.
Wallafawa ranar:
A wani jawabi da ya yi ta kafar bidiyo, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce duk da haka Rasha ba ta da juriyar da karfin gwiwar yin nasara a kan kasarsa, illa tinkaho da take da dimbim makamai da take da su.
Mataimakiyar Firaministan Ukraine Iryna Vereshchuk ta ce dakarun Rasha sun tare wani ayari da ke tafiya da kayayyakin agaji zuwa birnin Mariupol a wani shingen bincike, amma tana fatan a yau Lahadi a kyale ayarin ya isa birnin.
Wani jami’i a Ukraine ya ce dakarun Rasha sun yi luguden wuta a wani wurin atisayen soji a birnin Lviv da ke yammacin kasar, birnin da dimbim masu neman mafaka daga rikicin suka shiga a makon da ya gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu