Isa ga babban shafi
Gabashin Turai

Hare-haren Rasha sun dakile aikin kwashe fararen hula daga Mariupol - Ukraine

Mataimakin Firaministan kasar Ukraine Iryna Vereshchuk, ya ce harin da Rasha ke kaiwa kan Mariupol  ya hana aikin kwashe 'yan gudun hijira daga birnin mai tashar jiragen ruwa na Ukraine.

Wani yanki a birnin Mariupol na kasar Ukraine, bayan hare-haren da dakarun Rasha suka kai da manyan makamai.
Wani yanki a birnin Mariupol na kasar Ukraine, bayan hare-haren da dakarun Rasha suka kai da manyan makamai. © Ukraine/Handout via REUTERS
Talla

A cikin wani jawabi da ya yi ta kafar bidiyo, Vereshchuk ya ce an samu nasarar kwashe wasu mutane akalla dubu 1,000 daga kauyen Vorzel da ke Kiev babban birnin kasar ta Ukraine.

Bayanai sun ce sojojin Rasha da suka dakatar da wasu motocin bas na mutanen da ke kokarin tserewa daga yankin Kyiv, sun yi wa birnin Mariupol kawanya.

Kawo yanzu fararen hula dubu 1 da 582 suka rasa rayukansu a Ukraine tun bayan farmakin da Rasha ta kai kan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.