Isa ga babban shafi
Ukraine - Rasha

Zelensky ya ce Rasha ta tafka asara a Ukraine

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce  aikin tura karin dakaru zuwa kasarsa da Rasha ke yi na nuni da dimbim asarar da ta yi a yayin samamen da ta kaddamar, yana mai bayyana ta a matsayin asara mafi girma da Rasha ta taba fuskanta a cikin gwamman shekaru.

Volodymyr Zelensky, shugaban Ukraine.
Volodymyr Zelensky, shugaban Ukraine. AFP - HANDOUT
Talla

Zelensky ya kuma ce ya gana da shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz da shugaban Faransa Emmanuel Macron a kan su kara matsa wa Rasha lamba ta saki magajin garin  birnin Melitopol,  da ake zargin ta yi awon gaba da shi a ranar Juma’a.

A wani jawabi da ya gabatar ta kafar talabijin, Zelensky ya bukaci Rasha da ta mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta don a samu sukunin kwashe fararen hula a birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa da ta wa kawanya.

Rahotanni daga biranen Donestk da Kyiv na cewa Rasha na ci gaba da luguden wuta musamman ma a wuraren da ake aikin kwashe fararen hula, kamar yadda gwamnonin yankunan suka bayyana a mabanbantan sanarwai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.