Isa ga babban shafi
Turai - korona

Kasashen Turai na shirin hana mutanen da basu karbi rigakafi ba yawo

Sakamakon karuwar adadin masu harbuwa da annobar korona da ya kai wani sabon matsayi, gwamnatoci a Turai da wasu sassan duniya na shirin hanawa mutane da basu karbi rigakafin cutar ba walwala.Matakin da masu sukar lamarin ke kallo tamkar rashin adalci ne da kuma tilastawa jama’a karbar rigakafin.

Wani dauke da shaidar allurar rigakafin korona a kasar Italiya
Wani dauke da shaidar allurar rigakafin korona a kasar Italiya AP - Andrew Medichini
Talla

Australia na gab da ɗaukar matakin, inda ake saran majalisar kasar ta yi muhawara a karshen wannan mako wanda zai ba da umarnin hana mutanen da ba su sami allurai biyu na rigakafin ba fita ba gaira ba dalili da kuma mutanen da suka warke daga cutar.

Yunkurin ya kasance martani ne ga karuwar adadin masu kamuwa da cutar cikin sauri.

Tuni wasu jihohin Austria da Salzburg suka amince da matakan kulle ga wadanda ba a yi musu allurar ba, dokar da zata fara aiki daga ranar Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.