Isa ga babban shafi
aMURKA - CORONAVIRUS

Amurka za ta ba da ƙarin tallafin allurar rigakafin Korona miliyan 500 ga duniya

Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da shirin kasar na bada tallafin alluran rigakafin cutar Korona samfurin Biontech da Pfizer ga sauran kasashen duniya, inda yce yanzu Amurka ta bada tallafin jimillar alluran rigakafin Korona guda biliyan 1 da Miliyan 1.

Shugaban Amurka Joe Biden yayin da yake karban allurar rigakafin korona.
Shugaban Amurka Joe Biden yayin da yake karban allurar rigakafin korona. France24Screenshot
Talla

Biden wada ya sanar da wannan bayani ta wani jawabi da ya yi ta kafar bidiyo, ya ce burin kasar Amurka shine nan da watan Satumbar badi kowacce kasa ta yiwa kaso 70 cikin dari na al’ummar ta allurar.

A jawabin da ya yi wa taron majalisar dinkin duniya, shugaba Biden ya ce kasar ta narka dala biliyan 15 wajen samarwa duniya alluran.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta koka kan yadda kamfanonin samar da alluran rigakafin ke sanya bukatar samun riba a gaba fiye da rayukan mutane.

Kungiyar ta ce babban tashin hankalin shine yadda kasashe matalauta ke bukatar akalla allura biliyan biyu nan da karshen shekarar da muke ciki.

A cewar kungiyar, kamfanonin samar da alluran irin su AstraZeneca da BioNtech da Johnson and Johnson  da Moderna da Novava da Pfizer, sun yi kememe wajen tallafawa al’ummar duniya da alluran da kuma hana wasu fasahar da za’a yi amfani da ita wajen samar da allurar.

Ya zuwa yanzu dai tuni aka yiwa al’ummar duniya biliyan 6 allurar rigakafin cutar, kuma na sanya ran nan da kwanaki 29 a kara yawan alluran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.