Isa ga babban shafi
Turai-Coronavirus

Kashin 70 na al'ummar Turai sun yi rigakafin Korona

Shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce, an yi wa kashi 70 na balagaggun mutanen nahiyar allurar rigakafin Korona, abin da ke nufin cewa, kungiyar ta EU ta cimma muradinta.

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen,
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, Stephanie Lecocq POOL/AFP/Archivos
Talla

A wani hoton bidiyo da aka watsa a shafin intanet, Von der Leyen ta ce, a yau Talata, sun cimma wani gagarumin muradi a shirinsu na rigakafin Korona, domin kuwa kashi 70 na balagaggun mutanen kasashen Turai sun karbi rigakafin, abin da ke nufin cewa, kimanin mutane  miliyan 250 sun samu cikakkiyar kariya daga annobar.

Von der Leyen wadda ke jagorantar Hukumar Tarayyar Turai da alhakin sayo alluran rigakafin Korona ya rataya a wuyanta, tun a cikin watan Yulin da ya gabata, ta sanar cewa, kashi 70 na balagaggun sun karbi akalla zangon farko na rigakafin.

Yanzu haka kasashen duniya sun zafafa yunkurinsu na ganin sun ci galabar sabon nau’in cutar Korona samfurin Delta mai cike da hatsarin gaske.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa, wannan annoba ta Korona za ta iya kashe karin mutane dubu 236 a nahiyar Turai kadai nan da farkon watan Disamba, yayin da ta bayyana damuwa kan jan-kafa a shirin rigakafin Korona a nahiyar.

Korona dai ta kashe mutane akalla miliyan 4 da dubu 507 da 823 a duniya tun bayan barkewarta a cikin watan Disamban 2019 a China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.