Isa ga babban shafi
Faransa-Sarkozy

Sarkozy zai kalubalanci hukuncin daurin da kotun Faransa ta zartas masa

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy zai daukaka kara kan hukuncin daurin shekaru 3 da kotun Paris ta zartas masa jiya Litinin bayan samunsa da hannu dumu-dumu a badakalar rashawa.

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy.
Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy. AP - Michel Euler
Talla

Lauyan Sarkozy Jacqueline Laffont wadda ta bayyana hukuncin kotun a matsayin mai cike da rashin adalci ta ce hankalin tsohon shugaban mai shekaru 66 bai tashi ba kuma a shirye ya ke ya daukaka kara don kalubalantar hukuncin.

A jawabinta ga manema labarai bayan hukuncin da ya mayar da Sarkozy na biyu a jerin tsaffin shugabannin Faransa da almundahanar kudi ta jefa yari, lauya Laffont ta ce ko shakka babu suna da kwarin gwiwar kalubalantar hukuncin tare da bayyanawa Duniya cewa Nicolas Sarkozy bai aikata laifukan da ake tuhumarsa ba.

Sarkozy wanda ya shugabancin Faransa daga 2007 zuwa 2012, zai shafe shekara guda na hukuncin shekaru ukun ne a yari yayinda shekaru 2 zai karasa su a gida, bayan samunsa da hannu dumu-dumu a badakalar kudade baya ga amfani da kujerarsa wajen aikata ba daidai ba, ciki har da karbar makudan kudade daga hannun wani alkali don samar masa gwaggwaban aiki a Monaco.

Baya ga Sarkozy hatta lauyoyinsa sai da suka samu nasu hukuncin daurin a yari da suka hadar da Thierry Herzog da kuma alkali Gilbert Azibert bayan samunsu da laifin kokarin baiwa masu shigar da kara cin hanci don boye hujjojin da za a gabatar kan tsohon shugaban game da zargin da ake masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.