Isa ga babban shafi
Amurka - Trump

Zan sake takara a 2024 kuma zan doke Democrat - Trump

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sha alwashin sake tsayawa takarar shugabancin kasar a shekarar 2024, tare da ikirarin samun gagarumar nasara kan jam’iyyar Democtrat.

Tsohon shugaban Amurka Donnald Trump yayin jawabin na farko tun bayan barin sa mulki
Tsohon shugaban Amurka Donnald Trump yayin jawabin na farko tun bayan barin sa mulki REUTERS - OCTAVIO JONES
Talla

Tsohon shugaban Trump, ya sha alwashin sake kwato kasar amurka daga hannun ‘yan jam’iyyar ta democrats, inda ya ce ya zama wajibi ya ceci amurkan.

Donald Trump ya yi wadannan kalamai ne ta cikin jawabin farko da ya gabatar a filin taro dake Orlando tun bayan barin sa fadar white house a ranar 20 ga watan janairun da ya gabata.

Ta cikin jawabin nasa Donald Trump ya kuma sake jadadda cewa shine hakikanin wanda ya lashe zaben amurkan, amma ba Joe biden ba, tare da jefa kalaman gargadi ga wasu ‘yan majalisa 10 da suka kada kuri’ar neman tsige shi daga mukamin sa.

Shugaba Trump ya kara da cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen sake kwato fadar white house.

A yayin jawabin nasa wajen taron, Trump ya kuma yi watsi da jita-jitar cewa zai yi amfani da karfin magoya bayan da ya ke da su wajen kirkirar sabuwar jam’iyya.

Yace " Ba zamu sake kirkirar wata jam’iyya ba, muna da republican kuma zata ishe mu wajen sake karfarar mu da kuma hada kan ‘yan amurka fiye da ko yaushe"

Ta cikin jawabin da ya kwashe tsahon mintuna 90 yana gudanarwa, Trump ya kuma dage kan yin duk mai yiwuwa wajen dakatar da kwararar ‘yan ci rani zuwa kasar, yana mai Allah wadai da tsare-tsaren shugaban kasar Joe Biden kan sauyin yanayi.

A yayin taron dai an gudanar da wata kwarya-kwaryar kada kuri’a da ke neman ra’ayin jama’a game da sake tsayawa takarar Trump a shekarar 2024 wanda kuma akalla mutane 7 cikin goma wato kaso 55 na mahalarta taron suka nuna sha’awar ya sake tsayawa takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.