Isa ga babban shafi
Amurka-Trump

Trump ba zai iya sake neman shugabanci ba- Nikki Haley

Tsohuwar Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya lokacin mulkin shugaba Donald Trump Nikki Haley ta ce tsohon shugaban ba zai sake tsayawa takarar neman shugaban kasa ba, kuma kuskuren ‘yan Jam’iyyar Republican suka yi wajen gabatar da shi da kuma goya masa baya a zaben shekarar da ta gabata.

Nikki Haley a wata ganawarta da tsohon shugaban Amurka Donald Trump.
Nikki Haley a wata ganawarta da tsohon shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Haley wadda ta yi suna wajen goyan bayan tsohon shugaban kasar ta bayyana matukar damuwa kan abubuwan da suka biyo bayan shan kayen zaben da Trump ya yi daga hannun shugaba mai ci Joe Biden.

Tsohuwar jami’ar diflomasiyar ta ce bata jin Trump zai sake neman shugabancin Amurka, saboda halin da ya samu kan sa.

Haley ta kuma cacaki ‘ya'yan Jam’iyyar su ta Republican da suka goyawa tsohon shugaban baya wajen kalubalantar sakamakon zaben da ya sha kaye, abinda ya kai ga harin da magoya bayan sa suka kai Majalisar dokoki ranar 6 ga watan Janairu.

Tsohuwar jami’ar ta ce ya zama wajibi su nunawa Trump cewar ya basu kunya, domin ya kama hanyar da ba ta dace da shi ba, saboda haka ba za su bi shi ba, kuma bai dace su saurare shi ba.

Haley ta ce ita da kanta ta na nazarin shiga takarar shugaban kasa a shekarar 2024, kuma tun ranar 6 ga watan jiya bata yi magana da tsohon shugaban kasar ba.

Ta kuma bayyana cewa magoya bayan Trump da suka goyi bayan zargin da ya ke cewar an masa magudi, na bukatar wayar da kan su, domin an cika musu ciki da karairayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.