Sanatocin Amurka sun amince a ci gaba da shari'ar tsige Trump
Majalisar dattawan Amurka ta kada kuri’ar amincewa a ci gaba da sauraron bahasin tsige tsohon shugaba Donald Trump a karo na biyu, tana mai watsi da bayannin lauyoyi masu kare shi na cewa ya saba wa tsarin mulki.
Wallafawa ranar:
‘Yan majalisar 56, ciki har da ‘yan jam’iyyar Republican 6 ne suka amince Trump ya gurfana a gabansu don ya kare kansa daga laifin da ake tuhumarsa da aikatawa, a yayin da 44 suka zabi akasin haka.
Lauyoyin da ke kare Trump sun yi bayanin cewa, bai kamata ya gurfana a gaban majalisar Dattawa don amsa tambayoyi a kan ingiza magoya bayansa su yi bore a ginin majalisun dokokin kasar na Capitol ba, duba da cewa ya bar karagar mulki, amma ‘yan majalisar dattawan suka yi watsi da hakan, ta wajen kada kuri’ar ci gaba da bin wannan’ bahasi.
An bude wannan lamari mai dimbim tarihi a zauren majalisar dattawan Amurka ne, a daidai lokacin da masu gabatar da kara suka sha alwashin yin galaba da kwararan shaidu da suke da su a kan harin da magoya bayan Trump suka kai wa ginin majalisun dokokin kasar, Capitol.
Duk da faya fayen bidiyo da masu gabatar da karar suka mika wa majalisar, aka kuma buga su, lauyoyin tsohon shugaba Trump sun dage cewa shari’ar tsigewa da ake neman yi wa ubangidan nasu ta saba wa kundin tsarin mulki kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu