Isa ga babban shafi
Chadi

Jami'an tsaro sun kashe mini mahaifiya da 'yan uwana - Yaya Dillo

Mahukuntan Chadi da wani babban dan adawa da ke neman shugabancin kasar  na zargin juna kan mummunan rikicin da yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu da jikkatar wasu biyar a Djamena babban birnin kasar a sanyin safiyar jiya Lahadi.

Dan adawar Chadi Yaya Dillo da jami'an tsaro suka farma gidansa a Djamena
Dan adawar Chadi Yaya Dillo da jami'an tsaro suka farma gidansa a Djamena AFP - THOMAS COEX
Talla

Gwamnatin kasar tace, mutune biyu sun mutu yayin da biyar suka jikkata a artabun da aka yi ranar Lahadi bayan da jami’an tsaro suka yi kokarin kama dan siyasar Yaya Dillo Djerou.

Yayin kare matakin yunkurin kama jagoran ‘yan adawar, kakakin gwamnatin kasar ta Chadi Sherif Mahamat Zene, yace jami’an tsaro na gaf da shiga gidan Yaya Dillo ne, wasu mutane da ake kyautata zaton magoya bayan sa ne suka bude musu wuta, abinda ya tilasta musu maida martani domin kare kai, kuma cikin wadanda suka jikkata har da jami’an tsaro uku.

Sherif ya kuma caccaki jagoran ‘yan adawar bisa baiwa magoya bayansa umarnin daukar makamai domin bashi kariya, duk da cewar sau biyu Kotu ke aike masa da sammaci.

To sai dai sa’o’i kafin barkewar fadan tsakanin magoya bayansa da jami’an tsaro, Yaya Dillo ya wallafa sako a shafinsa na Facebook dake cewa jami’an tsaron kasar sunyi wa gidansa kawanya tare da kashe mahaifiya sa da wasu ‘yan uwa.

Yaya Dillo tsohon dan tawaye ne, kuma yayi minister karkashin gwamnatin shugaba Idris Deby Itno, kuma a ranar Jumma’a ya cika takardun tsayawa takarar neman shugabancin kasar a zaben da ke tafe na watan Afrelu, inda Deby dake Mulki tsawon shekaru 30 ke neman tazarce a karo na shida.

Yanzu haka dai Dillo na fuskantar tuhume-tuhume har kashi biyu, ciki har da cin zarafi, da kuma bata sunan Uwargidan shugaban Chadi Hinda Beby Itno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.