Isa ga babban shafi
Faransa-Sarkozy

Kotun Faransa ta aike da tsohon shugaban kasar gidan yari na shekaru 3

Kotun Faransa ta aike da tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy gidan yari na shekaru 3 bayan karkare shari’ar da ake masa a yau, wadda ta same shi da hannu dumu-dumu a laifukan rashawa da almundahanar kudi.

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy bayan zartas masa da hukuncin daurin shekaru 3 a yari, yau Litinin.
Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy bayan zartas masa da hukuncin daurin shekaru 3 a yari, yau Litinin. AFP - ANNE-CHRISTINE POUJOULAT
Talla

Hukuncin na shekarun 3 kamar yadda alkalin ya zartas kan Sarkozy ya nuna cewa tsohon shugaban kasar zai yi zaman yari na shekara guda yayinda zai karasa wa’adin shekarunsa 2 waje, kwatankwacin wanda aka zartaswa ubangidansa a siyasa Jacques Chirac wanda shima ya taba karbar hukuncin shekaru 2.

Shari’ar wadda ta gudana a birnin Paris na nuna cewa Sarkozy na da zarafin iya daukaka kara kan batun ba kuma tare da barazanar kame daga jami’an taro ba, dai dai lokacin da tsohonn shugaban ke mafarkin dawo da martabarsa har ma da sake tsayawa takara a kasar ta Faransa.

Sarkozy mai shekaru 66 wanda ya shugabanci Faransa daga 2007 zuwa 2012 kuma ya ke da miliyoyin magoya baya har zuwa yanzu, kotun ta sameshi da laifin amfani da karfin kujerarsa wajen aikata ba dai dai ba yayin mulkinsa sai kuma karbar rashawa.

Sauran laifukan da Sarkozy ya aikata sun hada da karbar na goro don karawa ma’aikata mukamai ciki har da wani alkalin da ya taimakawa samun gwaggwaban aiki a Monaco.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.