Isa ga babban shafi
Faransa-Rwanda

Faransa ta taimaka wa masu hannu a kisan Rwanda-Kundin ajiya

Wani kundin diflomasiya ya bayyana cewa, hukumomin birnin Paris sun taimaka wa mutanen da ake zargi da hannu a kisan kiyashin Rwanda tserewa bayan sun kasance a tsare a hannun sojojin Faransa. Wannan al’amari ya kara tabbatar da zargin da gwamnatin Rwanda ta yi na cewa, Faransa ta goyi bayan dakarun Hutu wajen aiwatar da kisan a shekarar 1994.

Tsohon shugaban kasar Faransa Francois Mitterand da ke matsayin shugaba a wancan lokaci da ake zargin Faransar ta taimakawa makasan Rwanda.
Tsohon shugaban kasar Faransa Francois Mitterand da ke matsayin shugaba a wancan lokaci da ake zargin Faransar ta taimakawa makasan Rwanda. AFP PHOTO JEAN-CLAUDE DELMAS
Talla

Takardun da wani jakadan Faransa a Rwanda ya rubuta wadanda kuma Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya samu kwafinsu daga wani Lauya mai bincike kan kisan kiyashin, sun nuna cewa, hukumomin Paris na da masaniyar cewa, wadanda ake zargin sun nemi mafaka a tudun-mun-tsirar da ke karkashin kulawar sojojin Faransa.

A cikin watan Yunin shekarar 1994 ne, sojojin na Faransa suka isa Rwanda karkashin aikin Majalisar Dinkin Duniya da zummar dakatar da kisan kare-dangin da ya lakume rayukan mutane akalla dubu 800, akasarinsu ‘yan kabilar Tutsi marasa rinjaye.

Yannick Gerard, Jakadan Faransa a Rwanda, ya rubuta wa magabatansa takarda, inda ciki ya ke tambayar su kan abin da ya dace a yi wa mutanen da ake zargi da kisan kiyashin kamar dai yadda aka bankado daga wani tsohon kundin ajiya na mashawarcin shugaba Francois Mitterrand da ke shugabancin Faransa a wancan lokaci.

A cikin takardun, Mr. Gerard ya rubuta cewa, ba su da wani zabi illa kama wadannan mutane ko kuma a yi musu daurin talala don dakon matakin da hukumomin shari’a na kasa da kasa za su dauka.

A martanin da ya suka mayar masa, Hukumomin Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa sun shaida wa Gerard cewa, ya na iya amfani da hanyoyin sanayyarsa a nahiyar Afrika ba tare da ya fallasa kansa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.