Isa ga babban shafi
aFRI

Faransa za ta bayar da dama na sake leka kundaye yakin Rwanda

Faransa ta bakin tsohon Firaminstan kasar Edouard Balladur ,ta ce za ta baiwa jama’a damar leka kundayen yakin Rwanda na shekara ta 1994,yakin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 800.000 a lokacin.

Edouard Balladur tsohon Firaministan Faransa
Edouard Balladur tsohon Firaministan Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

Tsohon Firaministan Faransa Edouard Balladur  nan gaba jama'a za su fahimtar abinda ya faru a Rwanda ,dama irin rawar da kasar sa Faransa ta taka a shekara ta 1994.

Tsohon Firaministan Faransa ya na mai cewa ya dau niyar kawo karshen sirin dake tattare da rikicin kasar na Rwanda domin baiwa kowa damar sanin ainayin abinda ya faru a lokacin da ya rike mukamin Firaministan Faransa kama daga shekara ta 1993 zuwa 1995.

Tsohon jami’in gwamnatin Faransa na cigaba da nuna goyan bayan sa ga kasar sa musaman rawar da ta taka a lokacin a karkashin shugabancin Francois Mitterand.

Edouard Balladur ya na mai yabawa rundunar da aka tura a lokacin domin wanzar da zaman lafiya,yayinda wasu ke ci gaba da nuna adawa da tsarin ,wanda ake dangata shi da abinda ya rusa zaman lafiya ga baki daya a kasar ta Rwanda tareda baiwa wasu kungiyoyi dake dauke da makamai damar cin karne su ba babaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.