Isa ga babban shafi
faransa

Fitaccen mawakin Faransa ya rasu yana da shekaru 94

Fitaccen mawakin Faransa, Charles Aznavour wanda a makon jiya ya ce, ya yi mafarkin cewar zai yi numfashinsa na karshe a dandalin rawa, ya rasu yana da shekaru 94 a duniya.

Marigayi Charles Aznavour
Marigayi Charles Aznavour RFI / Edmond Sadaka
Talla

Mai magana da yawunsa tace, Aznavour wanda bai dade da dawowa daga kasar Japan in da ya gudanar da kade-kade ba, ya rasu ne a gidan sa dake Alpilles da ke kudu maso gabashin Faransa a ranarv Litinin.

Ana kallon marigayin a matsayin wani babban gwani musamman idan aka yi la’akari da fasahar da Allah ya hore masa ta rubuta wakoki da kuma rera su.

Tuni shugaban Faransa ya jagoranci al’ummar kasar wajen mika sakon ta'aziya na rashin Aznavour wanda ya soke gudanar da kade-kade da dama a bara sakamakon karayar da ya samu a hannunsa.

Shugaba Macron ya jinjina wa fasahar marigayi Aznavour.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.