Isa ga babban shafi
Amurka

Fitacciyar mawakiyar Amurka Aretha Franklin ta mutu

Fitacciyar mawakiyar Amurka da ake yi wa lakabi da Queen of Soul, Aretha Louise Franklin ta mutu tana da shekaru 76 a gidanta da ke birnin Detroit bayan fama da cutar daji ko kuma Kansa. Tuni shugaban Amurka, Donald Trump da Barack Obama da Bill Clinton da Hillary Clinton suka jinjina wa marigayiyar kan rawar da ta taka wajen nishadantar da al’umma.

Aretha Franklin ta shafe shekaru 60 tana jan zarenta a masana'antar wakoki ta Amurka
Aretha Franklin ta shafe shekaru 60 tana jan zarenta a masana'antar wakoki ta Amurka © Donaldson Collection/Michael Ochs Archives/Getty Images
Talla

Marigayiyar wadda ta lashe kyautar Grammy har sau 18 ta shafe kimanin shekaru 60 tana jan zarenta a masana’antar wakoki ta Amurka, in da wakokinta suka yi tasiri wajen janyo hankulan mata ‘yan uwanta shiga harkokin waka kamar su Mariah Carey da Whitney Houston da Alicia Keys da Beyonce da Mary J. Blige da kuma Amy Winehouse.

Mujallar Rolling Stone ta bayyana Aretha Franklin a matsayin daya daga cikin fitattun mawaka 100 da suka fi shahara a tarihin duniya.

Franklin ta rera wakoki a yayin bikin rantsar da shugabannin Amurka da suka gabata da suka hada da Bill Clinton da Barack Obama.

A shekarar 2005 ne gwamnatin Amurka karkashin shugabancin George W. Bush ta karrama Franklin da lambar yabo mafi girma da fadar shugaban kasa ke bai wa fararen hula.

A shekarar 2010 marigayiyar ta fara fama da matsanancin rashin lafiya amma duk da haka ta ci gaba da rera wakoki har zuwa karshen shekarar bara, lokacin da ta yi wa gidauniyar Elton John da ke yaki da cutar Kanjamau, waka a birnin New York, kuma a bara din ne birnin Detroit ya sanya wa wata unguwa sunanta.

Za a ci gaba da tuna marigayiyar da wakokinta irinsu Respect da Natural Woman da I say a Little Prayer da Day Dreaming da Jump to It da Freeway of Love da A Rose Is Still a Rose da I Knew you Were Waiting For Me.

Iyalanta sun ce nan da ‘yan kwanaki masu zuwa za su sanar da ranar gudanar da jana’izarta, yayin da suka mika sakon godiya ga magoya bayanta a sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.