Isa ga babban shafi
Faransa

Fitaccen mawakin Faransa Hallyday ya rasu

Shahararren mawakin kasar Faransa Johnny Hallyday ya rasu a cikin daren jiya yana da shekaru 74 a duniya.

Marigayi Johnny Hallyday
Marigayi Johnny Hallyday REUTERS/Charles Platiau
Talla

Halliday da ya share sama da shekaru 50 yana waka, ya mutu ne sakamakon fama da cutar kansa da ta kama huhunsa.

Marigayin ya siyar da kimanin kwafi miliyan 100 na faya-fayen wakokinsa kuma ya haska a wasu fina-finai tun daga shekarar 1960.

Tsohon shugaban Faransa Jacques Chirac ya karrama Hallyday da babbar lambar yabo ta kasa a shekarar 1997 saboda gudun mawarsa a fannin nishadantar da al’umma.

Marigayin ya yanke shawarar shiga harkar waka ne bayan ya kalli hoton bidiyon wakar Elvis Presley ta kafar talabijin a shekarar 1957.

Hallyday ya kware a salon wakar Rock and Roll kuma shi ne ya dabbaka salon a Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.