Isa ga babban shafi
Ukraine

Dangin fasinjan jirgin MH17 sun yi bidiyon jan hankali

Dangin fasinjan jirgin MH17 da suka mutu wanda aka kakkabo a gabashin Ukraine yau tsawon shekaru uku, sun fitar da wani hoton bidiyo domin janyo hankalin duniya ga halin da suke ciki.

Tarkacen jirgin Malaysia MH17 da aka harbo a Ukraine.
Tarkacen jirgin Malaysia MH17 da aka harbo a Ukraine. AFP/AFP/Archives
Talla

Masu binciken faduwar jirgin da ake zargin ‘Yan tawayen Ukraine ne suka harbo, na fatan Bidiyon zai janyo hankalin mutanen yankin da jirgin na Malaysia MH17 ya fadi domin su fito su gabatar da sheda.

Bidiyon na kunshe ne da tattaunawa da mutane biyu cikin dangin fasinjan jirgin 298 da suka mutu bayan kakkabo jirgin daga sama da wani babban makami mai lizami kirar Rasha a ranar 17 ga watan Yulin 2014.

An yi bidiyon ne da nufin yanyo hankalin duniya bayan shafe shekaru uku ba wani hukunci ko diyya.

Bidiyon na dauke da jimami da radadin da wata uwa ke ciki da ta rasa danta, kuma masu bincike na fatar bidiyon zai janyo hankalin mutanen yankin da jirgin da ya fadi domin su fito su bayar da shedu

Yawancin dai fasinjan jirgin yan kasar Holland ne, sannan binciken da aka kammala ya tabbatar da cewa harbo jirgin aka yi.

Akwai mutane sama da 100 da ake bincike kan alaka da harbo jirgin, kuma bincike ya tabbatar da cewa an harbo jirgin ne daga yankin da ke ikon ‘yan tawayen Ukraine masu da’awar Rasha.

Sai dai Rasha ta yi watsi da rahoton binciken.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.