Isa ga babban shafi
Malaysia

Za a hukunta masu hannu a harbo jirgin MH17

Fimiranistan Malaysia, ya ce kasar za ta dauki dukkanin matakan da suka wajaba domin hukunta wadanda suka harbo jirgin saman fasinjar kasar lokacin da yake ratsa sararin samaniyar kasar Ukraine, in da aka samu asarar rayukan mutane 298 da ke cikinsa kimanin shekaru biyu da suka gabata.

Buraguzan jirgin MH17 da ya yi hatsari dauke da mutane 298
Buraguzan jirgin MH17 da ya yi hatsari dauke da mutane 298 AFP/AFP/Archives
Talla

Firaminista Najib Razak, na mayar da martani ne bayan da wani rahoto da masu bincike suka fitar ya tabbatar cewa, makami mai linzamin da aka yi amfani da shi wajen harbo wannan jirgi, an shigo da shi ne daga Rasha, kuma ana zargin mutane akalla 100 da hannu wajen taimakawa a harbo jirgin.

Makamin samfurin BUK wanda kasar Rasha ce kawai ke kera irinsa, masu binciken sun ce an harba shi ne daga wani yankin gabashin Ukraine da a lokacin yake karkashin kulawar ‘yan aware da ke samun goyon bayan Rasha.

Firmanistan kasar Netherlands da ta rasa mutane 196 daga cikin fasinjojin jirgi, Mark Rutte ya ce, kasar na fatan ganin an kafa wata kotun musamman ta kasa da kasa domin hukunta wadanda ake zargi da hannu wajen aikata wannan abin assha.

Bayan faruwar wannan lamari a shekara ta 2014, kasashen Turai da ke mara wa Ukraine baya a rikicinta da Rasha, sun sanya wa Moscow takunkumai saboda da abin da suka bayyana shi da cewa, kin bayar da hadin kai ne ga masu binciken musababbin lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.