Isa ga babban shafi
Malaysia

Za a dakatar da ci gaba da neman jirgin MH370

Kasashen Malaysia da Australia da kuma China sun ce akwai yiwuwar su dakatar da binciken da suke yi na hadin gwiwa don gano jirgin fasinjan Malaysia mai lamba MH370 idan har ba a samu wani ci gaba ba.

Za a dakatar da ci gaba da neman jirgin Malaysia mai lamba MH370 da baya bace shekaru biyu da suka gabata
Za a dakatar da ci gaba da neman jirgin Malaysia mai lamba MH370 da baya bace shekaru biyu da suka gabata REUTERS/Patrick Becot
Talla

Yanzu haka Ministocin sufuri na kasashen uku, sun fara taro don tattauna mataki na gaba game da ci gaban binciken.

A yayin taron da suka yi a birnin Putrajaya, Ministan sufurin Malaysia Liow Tiong Lai  ya ce, fatan ganin an gano jirgin fasinjan na dusashewa.

Liow ya ce muddin ba su samu wata cikkakiyar alama ta binciko jirgin ba, ya zama tilas a dakatar da binciken har sai abin da hali ya yi.

Wasu daga cikin iyalan fasinjojin da hadarin ya ritsa da su sun yi maraba da matsayar Ministocin duba da cewa ba a daina binciken za ayi ba.

Tun a ranar 8 ga watan Mayun 2014, jirgin na MH370 dauke da fasinjoji 239 ya bace a lokacin da ya ke kan hanyarsa daga Kuala Lumpur zuwa birnin Beijing na kasar China, daya daga cikin hadari mafi girma a tarihin sufuri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.