MH17: Rasha ta kalubalanci Amurka
Gwamnatin kasar Rasha ta kalubalanci Amurka akan ta fitar da hujjoji game da zargin an yi amfani da makami mai linzami aka harbo Jirgin Malaysia da ya tarwatse a yankin da ‘Yan a ware ke iko a kasar Ukraine. Mataimakin Ministan Tsaron Rasha Anatoly Antonov ya kalubalanci Amurka ta fito da hujjojin da tace tana da su akan an yi amfani da makami mai linzami daga gabacin Ukraine.
Wallafawa ranar:
Tuni, Amurka tace tana da bayanai na hujjoji da ta samu daga tauraron Dan Adama da suka nuna an yi amfani da makami mai Linzami aka harbo Jirgin Malaysia a ranar Alhamis din mako jiya inda dukkanin mutanen Jirgin suka mutu.
Kuma Amurka ta yi zargin cewa kasar Rasha ce ta ba ‘Yan tawayen Ukraine makamai domin yaki da gwamnatin Ukraine.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu