Isa ga babban shafi
Amurka

An bude wuta kan mutane a Washington

Jami’an tsaro a birnin Washington na kasar Amurka sun ce mutane biyar sun rasa ransu bayan bude wuta da akayi kan jama’a da ke hada hada a wani babban shagon saida kayayyaki da ke yankin Burlington.

'Yan sanda a Washington sun fara gudanar da bincike kan harin dan bindiga
'Yan sanda a Washington sun fara gudanar da bincike kan harin dan bindiga
Talla

Rundunar ‘yan sanda a birnin ta ce, ta baza komarta domin nemo wani mutum sanye da kaya ruwan toka, da na’urorin daukar hoto suka nada yana ficewa daga ginin bayan harin.

Har yanzu dai ba’a kai ga tantance yawan mutanen da suka samu raunuka ba a harin, kuma ba'a gano makasudin kai harin ba.

A kwanakin baya wasu daga cikin kasashen nahiyar turai sun fama da irin wannan hari, ciki akwai Faransa, da kasar Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.