Isa ga babban shafi
Amurka

Masu zanga-zanga sun bijire a North Carolina

Daruruwan masu zanga zanga sun bijire wa dokar hana fita da aka sanya a Charlotte da ke jihar North Carolina ta Amurka,  in da suke ci gaba da nuna bacin ransu kan yadda 'yan sanda suka harbe wani bakar fata har lahira.

Masu zanga zangar nuna bacin rai da kisan Keith Lamont Scott a jihar North Carolina ta Amurka
Masu zanga zangar nuna bacin rai da kisan Keith Lamont Scott a jihar North Carolina ta Amurka
Talla

Gwamnan Jihar ya kafa dokar ta baci dan kauce wa ci gaba da samun tahsin hankali, in da aka girke daruruwan jami’an tsaro, amma hakan bai hana mutane ci gaba da zanga zangar ba dauke da allunan da ke bukatar 'yan sanda su daina kashe su.

'Yan sandan sun ce, an harbe bakar fatar ne mai suna Keith Lamont Scott dan shakara  43 bayan ya dauki makami a lokacin da suka kai samame wani gida da nufin kama wani mutum mai laifi.

Sai dai dangin Scott sun musanta ikirarin 'yan sandan na cewa, yana dauke da makami, in da suka ce, littafi ne kawai a hannunsa.

Jama'a na ci gaba da matsin lamba don ganin jami'an 'yan sandan sun fitar da hoton bidiyon kisan Mr. Scott.

'Yan sanda dai na yawan harbe bakaken fata har lahira a kasar ta Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.