Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka na bincike kan hare-haren da aka kai kasar

Hukumomin Amurka sun kaddamar da bincike kan wasu hare-hare guda uku da aka kai a rana guda a biranen New York da New Jersey da kuma Minnesota don ganin ko suna da alaka da harin ta’addanci.

Amurka na gudanar da bincike kan hare-haren da aka kai kasar
Amurka na gudanar da bincike kan hare-haren da aka kai kasar REUTERS/Rashid Umar Abbasi
Talla

Hukumomin sun ce, ya zuwa yanzu babu wata shaida da ke nuna cewar, hare-haren na da alaka da juna, amma ganin yadda aka kai su cikin sa’oi 24 musamman na birnin New York,  in da shugabanin kasahsen duniya suka fara sauka don halartar taron Majalisar Dinkin Duniya, akwai fargaba.

Tuni dai aka tsare mutane biyar da ake zargi da hannu a lamarin, in da ake yi musu tambayoyi kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka rawaito.

Wani rahoto ya ce, bam din da ya tashi a New York ya yi kama da wanda ya tashi a Boston a shekarar 2013.

Akalla mutane 29 suka samu raunuka a harin na New York.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.