An sace bayanan mutane miliyan 500 a Yahoo
Kamfanin Yahoo ya bayyana cewa, masu kutse sun sace bayanan mutane kimanin miliyan 500 bayan sun yi nasarar shiga cikin akwatinsu na imel.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ana ganin dai wannan shi ne kutse mafi girma da aka yi wa jama’a a tarihin keta dokokin intanet a duniya.
Kutsen dai ya hada da satar sunayen mutane da adireshinsu da lambar wayarsu da ranakun haihuwarsu da kuma haruffan sirri har ma da
tambayoyi da amsoshi na sirri.
Tuni dai Hukumnar bincike ta Amurka FBI, ta fara gudanar da bincike game da kutsen wanda Yahoo ya ce, wasu jagorori ne suka dauki nauyin aikata haka.
Kamfanin na Yahoo ya bukaci masu amfani da shi da su sauya haruffansu na sirri matukar ba su yi haka ba tun shekarar 2014.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu