Isa ga babban shafi
Faransa

‘Yan Majalisa na adawa da dokar hana rike mukamin siyasa biyu

‘Yan majalisar Faransa kimanin 100 sun bukaci a dakatar da fara yin aiki da wata sabuwar doka da ta bukaci a hanawa ‘yan siyasar kasar rike mukamai biyu ko fiye da haka a lokaci guda.

Zauren Majalisar Faransa
Zauren Majalisar Faransa REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Da ma akwai dokar da ke haramta rike mukaman siyasa biyu ko fiye da haka a lokaci guda, sai dai ‘yan majalisar da suka sanya hannu kan wannan bukata sun bukaci a dakatar da fara yin aiki da dokar har zuwa shekara ta 2020.

Manazarta na ganin cewa dakatar da fara aiki da dokar zai taimaka wa tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy wanda ke rike da shugabancin jam’iyyarsa sannan kuma ya ke rike da wani mukamin siyasa a garinsa na asali.

A cikin makon da ya gabata ne ‘yan majalisa daga jam’iyyar Republican da Sarkozy ke shugabanta, suka gabatar da bukatar ganin a dakatar da fara yin aiki da dokar, inda ta samu goyon bayan ‘yan majalisar wakilai 99 yayin da wasu ‘yan majalisar dattawa 80 suka amince da ita.

A Faransa, yanzu haka akwai mutane da dama da ke rike da mukaman ‘yan majalisa, ministoci a lokaci daya da mukaman kansila ko kuma shugaban karamar hukuma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.