Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa : Mabiya Katolika na ibada cikin matakan tsaro

Dubban mabiya darikar katolika sun hada gangami a yau Litinin domin gudanar da hajjin Lourdes a yau Litinin, kuma ana gangamin ibadar ne cikin tsauraran matakan tsaro bayan kisan wani fada a watan da ya gabata.

Ministan cikin gida Bernard Cazeneuve à wajen ibadar Lourdes a Faransa
Ministan cikin gida Bernard Cazeneuve à wajen ibadar Lourdes a Faransa PASCAL PAVANI / AFP
Talla

Wannan ne karon farko da ake gangamin ibadar a wajen da ake kira haramin mabiyan na Katolika da ke lardin Lourdes a Faransa tun bayan kisan wani fada mai suna Jacques Hamel wanda Mayakan IS suka ma shi yankan rago.

Mabiya darikar katolika daga sassan Turai da gabas tsakiya da kuma yankin Asiya ne ke gudanar da ibadar a Lourdes, wanda yana cikin manyan hajjin mabiyan.

Sai dai ana gangamin ne cikin tsauraran matakan tsaro inda aka baza jami’an tsaro sama da 500 domin kare rayukan mabiyan sama da dubu ashirin da biyar.

kuma jami’an tsaron sai sun caje mabiyan kafin su shiga wajen ibadar domin gujewa wata barazana a gangamin.

An toshe hanyoyin zuwa wajen ibadar a Nice don kaucewa irin harin da wani ya danno babbar mota ya kashe mutane.

mabiya addinin na kirista yawancinsu sun ce sun zo ne Faransa domin gudanar da addo’in samun zaman lafiya a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.