Isa ga babban shafi
Isra'ila-Amurka-Falastine

Limaman Darikar Katolika sun kai Ziyara zirin Gaza

Wasu ayarin Limaman darikar Katolika daga kasashen Turai da Arewacin Amurka sun kai ziyara a yankin Zirin Gaza, inda suka sha alwashin ganin sun tursasawa Gwamnatocin kasashen duba lamarin fin karfin da Isra’ila ke yi a yankin.

Mujami'ar Katolika a Zirin Gaza
Mujami'ar Katolika a Zirin Gaza ©RFI/Nicolas Falez
Talla

Bayan ziyarar da suka kwashe kwanaki uku, manyan masanan Addinin Kirista sun halarci tarukan addu’o’i a Mujamu’ar Bethlehem da garin Beit Jalla da Madaba da Zarqa a yankin kasar Jordan.

Sun fadi cikin wata sanarwa bayan ziyarar cewa sun ji yadda wasu mazauna yankin ke kokawa game da yadda ake neman kwace masu gonaki da wuraren ibada.

Mazauna yankunan sun shaidawa Limaman cewa shingen da Israela ta yi, ya haifar masu da matukar cikas domin an yanke su da ‘yan uwansu da gonakinsu.

A shekara ta 2002 ne dai Isra’ila ta fara gina shinge, tare da kare abinta. Falestinawa na ganin wannan mamaya ne da fin karfi.

Kotun duniya dai ta yanke hukunci tun cikin shekara ta 2004 cewa a ruguza sassan da aka shiga yankin Falestinu, amma Isra’ila taki aiwatar da umurnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.