Isa ga babban shafi
Falestine

Mahmoud Abbas ya samu tarba daga dubban Falesdinawa

Dubban mutane ne suka tarbi shugaban Falasdinawa, Mahmud Abbas bayan samun nasarar daga darajarsu a Zauren Majalisar dinkin Duniya. ‘Mun samu kasa yanzu” inji Abbas ya ke shaidawa Daruruwan Falesdinawa a gabar yamma da Kogin Jordan.

Dubban Falasdinawa suna murna a lokacin da suke tarbar shugabansu Mahmoud Abbar bayan samun daraja a Majalisar Dinkin Duniya
Dubban Falasdinawa suna murna a lokacin da suke tarbar shugabansu Mahmoud Abbar bayan samun daraja a Majalisar Dinkin Duniya Reuters
Talla

A lokacin da ya ke jawabi ga taron Faledinawa, Shugaba Abbas yace Falasdinu ta kafa tarihi, yana mai fatar ganin an kawo karshen yadda ake musguna musu, da kuma gine gine a filayensu, Shugaban kuma ya bukaci hadin kan Falasdinawa don ci gaba da fafutukar su.

Kasashen Amurka da Isra’ila suna nan kan bakar sun wajen ci gaba da adawa da Falesdinawa.

A Ranar Juma’a Kasar Isra’ila ta bayyana kudirin gina sabbin gidaje 3,000 a yankin gabar Yamma da kogin Jordan da ke kusa da birnin Kudus.

Amma Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya yi gargadin cewar shirin kasar Isra’ila na gina sabbin gidaje 3,000 a Yankunan Falasdinawa zai rufe duk wata kofa na sasantawa da su.

Sanarwar da kakakin Sakatare Janar ya rabawa manema labarai ta nuna cewar, duk wani gini a Yankin na Falasdinwa haramtacce ne, kuma hakan zai yanke Birnin Kudus da Gabar Yamma da kogin Jordan.

Tuni kasashen Faransa Britaniya da kungiyar kasashen Turai da ma Amurka suka yi Allah wadai da shirin.

Bayan samun nasara a zauren Majalisar Dinkin Duniya Mahmoud Abbas yace babban abun da zai sa a gaba shi ne sasanta kungiyar Fatah da Hamas da ke shugabanci a Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.