Isa ga babban shafi
Palasdinu

Falasdinu ta samu shiga Majalisar Dinkin Duniya

Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da kasar Falasdinu a matsayin kasa mai sa ido, bayan gagarumin rinjayen kuri’u da ta samu, duk da adawar da Amurka da Isar’ila suka nuna. Kasashe 138 ne suka kada kuri’ar amincewa da bukatar da shugaban Palasdinwa, Mahmud Abbas ya gabatar, inda kasashe 9 suka ki amincewa, a yayin da 41 suka yi rowar kuri’un su.  

Wasu Falasdinawa dake murnar samun matsayin kasa mai sa ido a zauren Majalisar Dinkin Duniya
Wasu Falasdinawa dake murnar samun matsayin kasa mai sa ido a zauren Majalisar Dinkin Duniya mideastsolidarity.files.wordpress.com
Talla

Bayan zaben da aka kammala a daren jiya Alhamis, Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Suzan Rice, ta bayyana takaicin kasarta kan matakin da kasashen duniya suka dauka.

“Kudurin na yau mai cike da bakin ciki, zai kuma dawo da hannun agogo baya a yunkurin samar da zaman lafiya, ya jawo karin cikas kan matakan samar da zaman lafiya da aka dauko, shi ya sa Amurka ta ki amincewa da shi.”

 

Ta kara da cewa “abinda kudirin ke cewa shine ana neman a samar da ‘yantacciyar kasar Palasdinu mai cin gashin kanta, da za ta zauna lafiya da Isra’ila, mu ma haka muke so, sai dai mun dade muna fadin cewa hanya daya da za a samar da wannan, ita ce kawai ta bin hanya mai tsauri, amma mai muhimmanci, ta tattaunawa kai tsaye tsakanin bangarorin biyu.”
 

Tun a ranar Laraba Falasdinu ta fara ganin alamun nasarar cimma kudirinta na samun kujerar ‘Yan kallo a zauren Majalisar Dinkin Duniya saboda goyon bayan da suka samu daga kasashen Turai duk da Amurka da Jamus suna adawa da kudirin.
 

Faransa da Switzerland da Denmark sun ce za su kada kuri’ar amincewa da ‘Yancin Falasdinawa.
 

Falasdinawa dai sun yaba da matakin a kokarin da suke yi na neman samun goyon bayan kasashen Duniya a zauren Majalisar Dinkin Duniya.
 

Faransa ta fara bayyana goyon bayan Falasdinawa, kana wasu kasashen Turai suka bi sahu, amma Birtaniya ta ja da baya tana mai neman tabbacin Falasdinawa ba za su nemi kalubalantar Isra’ila ba a kotun Duniya kafin kasar ta amince da bukatarsu.
 

Kasar Jamus kuma a lokacin ta ce zata bi sahun Isra’ila da Amurka da ke adawa da Kudurin, tana mai cewa sahihiyar hanyar samun ‘yanci ita ce cim ma yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila.
 

A jiya Alhamis, Mahmoud ya gabatar da Jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya tare da janyo hankalin wakilan kasashen Duniya domin amincewa da kudirinsu.
 

Rahotanni sun nuna cewa kamin kada kuri’ar, Abbas ya gana da Manyan Jami’an diflomasiyar kasashen Duniya da suka hada da Ministan Harakokin wajen Turkiya wanda ya ba shi tabbacin za su amince da kudirin Falasdinawa.
 

Kasashen Rasha da China, da ke da kujerun din-din-din a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, sun dade suna bayyana shirin amincewa da bukatar ta Falasdinawa.
 

Dayawa ana tunanin cewa samun wannan dama da Falasdinawa suka yi zai basu damar shiga kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya, inda za su iya kai koke kan mamayar da Isra’ila ta yi a yankunansu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.