Isa ga babban shafi
Faransa

Mutane na gujewa biyan haraji a Faransa

Hukumar tattara haraji a Faransa ta karbi wata sanarwa mafi girma da ta girgiza ta, bayan bankado wasu bayanan sirri daga kasar Luxembourg na Asussun Ajiyar bankuna dubu 42 na ‘yan kasarta dake boye dukiyarsu domin kaucewa biyan haraji. 

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Charles Platiau
Talla

Ma’aikatar ajiya dake jihar Rhine Westphalia a kasar Jamus ce ta bankado bayyanan sirrin game asussun ajiya dubu 160 na kasashen Turai 19 dake boye kadarorinsu domin kauracewa biyan haraji.

Daga ciki asusu dubu 50 mallakar ‘yan kasar jamus ne, sai dubu 42 na faransa yayinda dubu 40 na yan kasar Belgium ne.

Ministan kudin kasar Norbert walter Borjans na Jam’iyyar SDP, yace ana cigaba da samun fallasar ire-iren wadannan asussun na kamfanoni da mutane dake tserewa haraji, lamarin dake haifar da koma baya ga bunkasar tattalin arziki a kasar Faransa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.