Isa ga babban shafi
Faransa

Air France na matsin lamba kan Ma'aikatansa

Kungiyar Ma’aikatan Jiragen Sama ta Kasar Faransa ta bayyana cewa Kamfanin Air France na ci gaba da matsin lamba kan ma’aikatansa dasu amince da saban shirinsa na sauye sauye, yayin da Kungiyar ta ce sauye sauyen zasu haifar da illa ga Ma’aikata.

Jirgin Air France
Jirgin Air France Guetty Images/ Pascal Le Segretain
Talla

Majiyoyin Kungiyar Ma’aikatan jiragen sun kara da cewa rage yawan jirage da kuma dakatar da Ma’aikata na cikin abubuwan da sabbin sauye sauyen suka kunsa.

A cewar Kungiyar, matukar sabbin sauye sauyen suka tabbata da yiwuwar Kamfanin ya dakatar zirgar zirgar jirage a hanyoyi 9 zuwa 14, yayin da ko wani jirgi daga cikin masu zirga zirgar a wadannan hanyoyin ke da ma’aikata a karkashinsa kimanin 350.

A watan mayun daya gabata ne Kamafanin Air France ya musanta labaran da aka yi ta yadawa a gidajen talabijin da sauran kafofi a duk fadin Kasar Faransa na cewa da ya na shirin koran ma’aikatansa dubu 3 da 300.

Kamfanin dai nata fafutukar ganin ya cimma matsaya game da shirinsa na sauye sauyen kafin karshen wannan wata na Satumba kuma har yanzu bai sasanta da wasu matuka jiragnesa ba daya samu sabani da su a baya sakamakon wadansu sauye sauye, inda ya bukaci rage wani kaso daga cikin kuadeden da ya kamata a basu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.