Isa ga babban shafi
Faransa

Air France zai gurfanar da Ma'aikatansa

Hukumomin kamfanin jiragen sama na Air France sun ce za a gurfanar da wasu ma’aikatan kamfanin 5 a gaban kotu, saboda mummunar zanga zangar da suka yi wadda ta kai ga yaga rigar daya daga cikin manyan Daraktocin kamfanin.

Air France zai gurfanar da ma'aikatansa saboda zanga zanga.
Air France zai gurfanar da ma'aikatansa saboda zanga zanga. REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Wani binciken cikin gida da aka gudanar ya nuna cewar ma’aikata 10 suka jagoranci zanga zangar, amma biyar daga cikin su ake shirin gurfanarwa a gaban kotu.

Kamfanin na neman sauya dokar aiki ne da zai sanya matukan jiragen tafiyar karin sa’oi 100 a cikin kowacce shekara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.